HANTSI, Kano Ayau Hausa

Hana Tashe a Kano: Matasa Uku sun Rasa Rayukan su

Matasan uku sun rasa rayukan su ne a unguwar Adakawa da ke birnin Kano, bayan hana tashe da hukumar ‘yan sanda tayi su kuma suka fito inda take ‘yan sandan da ake zargin na aiki a offishin ‘yan sanda na Jakara da sashen da ke yaƙi da ayyukan ‘yan daba ne suka bude musu wuta .
Rahotanni sun ce biyu da ga cikin matasan sun mutu nan take, ɗayan kuma bayan sun kamashi sun masa duka ya mutu, sai kuma ɗaya da suka harba a hannu wanda da yayi mummunan rauni a hannunsa.
Abba Hikima, shahararren lauyan nan na jihar Kano mai hanƙurin kare hakkin ɗan Adam ya bayyana takaicinsa da faruwar lamarin inda ya rubuta a shafinsa na Facebook kamar haka
“Yanzu don Allah a hankalce ya kamata ace a kokarin yan sanda na hana tashe an salwantar da rayukan jama’a? Na dauka kokarin kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a ne yasa aka hana tashen tun farko.
“Na karɓi korafe-korafe akan yadda yan sandan anti daba da jakara suka gudanar da ayyukan su a adakawa kuma idan bincike ya tabbatar da abun da ake zargi to lallai ɗaukar matakin Shari’a ya wajaba akan duk wanda aka samu da shiga hakkin jama’a a wannan wata” inji Abba Hikima.
Matakin rundunar ‘yan sanda na hana tashe a Kano baya rasa nasaba da ƙoƙarin ta na magance mugunyar ɗabi’ar nan ta masu ƙwacen waya waɗanda sau tari ke amfani da muggan makamai wajen yin aika-aikarsu, kamar yadda muka kalato daga AID Multimedia.

Leave a Reply