HANTSI, Kano Ayau Hausa

Menene Baraguzan Harsashi (Bullet Fragments)?

Daga Baqeer Mohammad Auwal

Duk da dai jahilai ne wawaye ke magana, amma saboda wayar da kan waɗanda basu sani ba. Shi harsashi ana ce mishi ammunition a turance, wato kafin a harba shi kenan. Ya na da sassa daban-daban, misali akwai case, kwanso kenan wanda ke rike da ɗan harsashin; shi ɗan harsashin shi ne sunansa bullet, in aka harba kwanson yana faduwa ƙasa ne sai dan ya tafi inda aka harba shi, wasu lokutan a dunkule yake zuwa, wasu lokutan ya na tarwatsewa ne, duk haka in ya tarwatse sunan waɗannan dalmumin baraguzan harsashi (bullet fragments). Kuma a haka za su watsu a jikin duk abinda su ka samu. Toh waɗannan barazugan (fragments) su ne ake magana a kai ba ɗan harsashi (bullet) ba, yadda na samu labarin irin harbin da aka yi wa Sheikh Zakzaky (H) barazugai 37 kamar kaɗan ne ma, sai dai da yake jiki baya son bakon abu, sannan kuma dalma (lead) ne shi ɗan harsashin, dalma kuwa ta na da illa a jikin ɗan Adam sosai, ƙwara ɗaya ma sai ta kai mutum lahira. Don haka Alhamdulillah da Allah ya so ya rayar da Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) duk da irin ta’addancin da hukumomin Nijeriya su ka aiwatar kansa. Ku kuma masu wauta, Allah ya tabbatar da ku cikin wautar, ya tashe ku a wawaye in kun mutu. –Baqeer Gashua ✍️23/02/2024.

Leave a Reply