HANTSI, Kano Ayau Hausa

‘Aisha Buhari ba ta nuna dattaku ba’

Daga Dr Aliyu Tilde

Gaskiya ban ji dadin da Hajiya Aisha Buhari ta ki sauraren rokon da ire-irena, da iyayen Aminu, da kungiyar dalibai, da jama’a da yawa suka mata ba kan cewa ta yafe wa yaron nan bayan ladabta shi da aka yi. BBC sun ce yau za a kai shi kotu.

Ai al’umma gaba daya ta roke ka ma arziki ne. Amma ka yi mirsisi ka ki ji kuma ba halin dattaku ba ne.

Ita kalmar “dattaku” da “dattijo” duk na Fulatanci ne. A Hausa muna ce masa halin girma.

A nan, abar kaunata ta kashe min gwiwa . Allah ya taimaka. 🙁

Don Allah jama’a banda zagi.

Dr. Aliyu U. Tilde
30 Nuwamba 2022.

Leave a Reply