HANTSI, Kano Ayau Hausa

Kotu ta dakatar da Almustapha daga takara

A yau Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar ta janye hukuncin da ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba na amincewa da ‘yan takarar da jagorancin Dr Adekunle Rufa’i Omo-Aje ya jagoranta na jam’iyyar Action Alliance (AA).

Mai shari’a Zainab Abubakar, a hukuncin da ta yanke, ta ce karar da Kenneth Obidiche Udeze ke jagoranta ya shigar ba ta da wani inganci.

Kamfanin dillancin labarai na Ƙasa ya rawaito cewa mai shari’a Abubakar a ranar 4 ga watan Nuwamba ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta amince da ƴan takarar da jagorancin Omo-Aje na jam’iyyar AA ya gabatar domin zaɓen 2023, kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.

Alkaliyar ta kuma umurci INEC da ta yi watsi da ‘yan takarar da shugabancin ɓangaren Udeze ya gabatar, daga cikinsu har da Manjo Hamzat Al-Mustpha (mai ritaya).

Amma Udeze, wanda aka amince da dakatarwarsa da kuma korar shi a matsayin shugaban AA na kasa a wasu hukunce-hukunce guda biyu na kotun daukaka kara, ya bukaci babbar kotun ta Abuja da ta janye hukuncin na ranar 4 ga watan Nuwamba, yana mai cewa an same shi ta hanyar zamba ne, kuma ya na da’awar cewa har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar na kasa.

Da ta ke yanke hukuncin a yau, Mai shari’a Abubakar, ta ce, bayan hukuncin kotun daukaka kara biyu da kuma wani hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a Abeokuta, Udeze ba zai iya yin ikirarin cewa shi ne shugaban jam’iyyar ba a bisa doka.

Hukunce-hukunce guda biyu na Kotun Daukaka Kara an yanke su ne a ranar 7 ga watan Janairu da 11 ga watan Nuwamba, yayin da kotun Abeokuta ta yanke hukuncin a ranar 8 ga watan Satumba, ƙarƙashin mai shari’a J. O. Abdulmalik a cikin wata kara mai lamba: FHC/AB/CS/120/2022.

Alkalin kotun ta ce hukuncin da ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba bai samu ta hanyar zamba ba kamar yadda Udeze ya yi zargi.

Ta bayyana Udeze a matsayin mutum ne mai cike da ruɗani kuma mai shiga tsakani, ya na kokarin tsoma baki a harkokin jam’iyyar da aka dakatar da shi daga bisani kuma aka kore shi.

Don haka Abubakar ta yi watsi da karar.

NAN ta ruwaito cewa Al-Mustapha, tsohon mai taimaka wa marigayi Janar Sani Abacha ne ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar da bangaren Udeze suka gudanar da jimillar kuri’u 506, inda ya doke Samson Odupitan wanda shi ne abokin hamayyarsa tilo a ranar 9 ga watan Yuni a Abuja.

Leave a Reply