HANTSI

Dakatar da Alkalin Alkalai: Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwa

Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwa kan matakin bangaren zartarwar Najeriya na dakatarwa da kuma sauya Alkalin Alkalan kasar.

Sanarwar da ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya fitar ta ce, Amurka ta damu sosai kan tasirin matakin da bangaren zartarwa ya dauka na dakatarwa da kuma sauya Alkalin Alkalai ba tare da goyon bayan majalisa ba yayin da babban zabe ke karatowa.

Sanarwar ta ce yadda matakin ya janyo suka game da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma ‘yancin bangaren shari’a, hakan na iya kawo cikas ga alkawalin da gwamnati da ‘yan takara da jam’iyyun siyasa suka yi na tabbatar da ganin an yi sahihi kuma karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.

Birtaniya ma ta bayyana damuwa kan dakatar da Alkalin Alkalan na Najeriya, inda ofishin jekadancin kasar ya ce matakin ya yi dab da lokacin zabe.

“Wannan zai iya cusa shakku a ciki da wajen kasar kan muradin gudanar da sahihin zabe a Najeriya”, in ji sanarwar.

A ranar Juma’a ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen tare da nada Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin na riko har sai an kammala shari’ar Onnoghen da ake tuhuma da kin bayyana dukiyar da ya mallaka kafin rantsar da shi a 2017.

Shugaban ya bayyana cewa kotun da’ar ma’aikata ce ta bayar da umarni a dakatar da shi har sai an kammala gudanar da shari’arsa.

Matakin dai ya janyo suka musamman daga bangaren ‘yan adawa da masana shari’a a Najeriya, inda wasu suka ce ya saba wa kundin tsarin mulki.

Amurka da Birtaniya sun bukaci a kawo karshen wannan dambarwar ta hanyar bin matakan da suka dace kuma cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply