GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Za mu bi wa Ummita hakkinta-Ganduje

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce za ta tabbatar da ganin shari’a ta yi aikinta a batun kashe Ummukhulthum Sani Buhari, matashiyar da ake zargin wani dan China da aikatawa.
BBC Hausa ta rawaito cewa Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, yayin wani jawabi a fadar gwamnatin jihar ya ce “Zub da jini (ne, don haka) dole maganar shari’ah ta shigo” kuma sai doka ta yi aikinta.
Ya ce tuni suka sa aka kama mutumin da ake zargi Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar ranar Juma’a.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne ran Juma’a da dare, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta mai da batun zuwa babban sashen binciken manyan laifuka bangaren kisan kai.
Mahaifiyar Ummita, Hajiya Lami Sani Buhari ta ce mutumin da ake zargi da kashe ‘yarta ya sha zuwa gidansu yana neman ganin Ummita, amma ba ta son fitowa.
Ta ce a ranar da lamarin ya faru, ɗan Chinan da ake zargi ya sake zuwa gidan da daddare inda ya yi ta buga musu kofa, abin da ya tilasta wa mahaifiyar bude masa kofa, don jin abin da ke tafe da shi.
Uwar ta ce Mista Geng ya bangaje ta, ya kutsa kai cikin dakin Ummita, kuma da ganin ta sai ya zare wuka ya yi ta caka mata.

Leave a Reply