GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Zan bar Najeriya fiye da yadda na same ta-Buhari

Shugaban Kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari ya ce yana da yakinin zai bar gida fiye da yadda ya same ta a shekarar 2015 da ya karbi karagar mulki.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ban-kwana ga ‘yan Najeriya, inda a ciki ya bayyana cewa ya yi duk mai yiwuwa a matsayinsa na dan Adam domin cika duk alkawuran da ya dauka ga ‘yan kasa.

Gobe Litinin ne Shugaba Buhari zai mika mulki ga sabon zababben Shugaban Kasa Cif Bola Ahmed Tinubu a filin Eagles Square da ke Abuja.

A shekarar 2015 ce Shugaba Buhari ya dare mulki bayan ya doke tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a lokacin da harkoki suke tabarbare matuka musamman harkokin tsaro.

Shugaba Buhari ya hau mulki ne bisa alkawarin magance rashawa da matsalar tsaro da inganta rayuwar mutanen kasa.

Sai dai a daidai lokacin da yake barin gado, ra’ayin ‘yan kasa ya rabu, inda wasu suke ganin ya yi kokari wasu kuma suke ganin bai tabuka ba.

Leave a Reply