HANTSI, Kano Ayau Hausa

Wani abu game da Mu’azu Magaji-Jafar Jafar

Daga Jafar Jafar
Akwai wani labari da na jima da sani, wanda duk wanda ya yi aiki da Kwankwaso a kusa-kusa ya sani.
Tun da Ganduje ya ke da Kwankwaso bai taba saka ma sa baki ba a wajen nada mukamai ba, face idan Kwankwason ya nemi shawararsa. A lokaci daya da Ganduje ya kasa daurewa, ya sa baki, shi ne lokacin da Kwankwaso ya nada Mu’azu a matsayin SSA.
A lokacin Ganduje ya hasala, ya sami Kwankwaso akan mai ya sa za a nada makiyinsa a mukami. Kwankwaso ya nuna wa Ganduje cewa ba don Muazu na kiyayya da shi ya nada shi, sai don ya ba da gudunmawa a gwamnatin. Haka dai Ganduje ya hakura, aka bar Muazu a SSA.
Allah da iko Ya ke sai ga shi daga baya Ganduje ya nada Muazu kwamashinan Ayyuka. Duk da cewa karatun Muazu ya kai a ba shi Kwamishinan Ayyuka, amma babban dalilin da ya sa a ka dankwalawa Muazu wannan babban kujera shi ne yana da bakin zage-zage da shirme da hauragiya a kan duk mai adawa da Ganduje. Amma da ya ke Muazun Muazun ne, har manyan hadiman Ganduje bai bari ba a hauragiyar da zage-zagen. Bayan ya yi kashi a nan, ya yi kashi a can, Ganduje dai ya gaji ya tallafi keyarsa.
Don Ganduje ya rufe masa baki, daga bisani sai ya nada shi shugaban kwamitin rangadi da zarwa a wajen binne bututun iskar gas ta AKK. Kamar yadda Shata ya fada, wato komai ka yi da dankama sai ya yi ma batun banza. Nan ma dai aka bazame shi.
Daga nan kuma sai ya bude sabon shafin adawa da zagin Ganduje. Allah Mai iko! Lamarin dai daga baya har sai da ya kai Muazu ga gidan kaso. Haka mu ka shiga mu ka fita, mu ka yi ruwa, mu ka yi tsaki — na manta da duk irin hauragiyar da ya yi min saboda Ganduje —sai da mu ka nemawa Muazu salama ya shaki iskar ‘yanci.
Bayan ya fito ya yi laushi, daga nan sai ya fara likewa su Shekarau a matsayin Autan Bawon Banza Bakwai. Nan ma da ya ga ba a yin komai da shi, sai ya shiga PDP tsagin Aminu Wali.
Muazu saboda tsabar rigima sai ga shi har da siyan fom din miliyoyi don yin takarar gwamna. Bayan ya sha kaye, kuma sun mayar da shi wani bi-ta-can, sai ya tafi wajen su Peter Obi. A nan ne fa su ka ba shi kafin alkalami na miliyan biyar da ya bude ofis ya kuma shiryawa jam’iyyar Labour Party gangami. Haka dai Muazu ya lamushe ya yi lumus.
Bayan ya manne a bayan dantakarar gwamna a jam’iyyar PDP wato Sadiq Wali don a dama da shi amma lamarin ya ci tura, sai ya hakura da cusa kai ba kwarjini ya fice daga PDP.
A yanzu dai Muazu ya koma jam’iyyar APC, wajen su Gawuna da Murtala da Abdullahi Abbas, wadanda babu irin cin mutunci da zagin da bai yi ma su ba a baya.
Allah Ya shiryi Muazu. Allah Ya ba shi lafiya.
© Jaafar Jaafar

Leave a Reply