Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa, Uncategorized

Ranar samun ’yancin kan Najeriya

Ranar 1 ga Oktoba ta kasance rana mai muhimmanci ga  Najeriya. A ranar ce aka sauke tutar Ingila, aka daga kore, fari da kore wato tutar Najeriya. A lokacin an yi murna da alfaharin samun ’yancin kai. Matasa kamar su Nnamdi Azikiwe da Herbert Macauly da Obafemi Awolowo da Sardauna Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa da Aminu Kano da Mudi Spikin da Sa’adu Zungur duk sun taka rawar gani wajen ganin wannan rana.

An fafata kafin Turawan mulkin mallaka suka bar Nahiyar Afirka.   A wasu kasashe sai da aka yi yakin sunkuru, wasu ma Turawa suka yi kaka-gida, inda suka mayar da ’yan asalin kasar bayi, marasa galihu, yayin da da kyar suka kwaci kansu!

An sadaukar da bauta don a samu ’yancin tafiyar da lamura, a lokacin an kawata fadoji da gidajen gwamnati da gadoji. An yi murna ganin irin burin da matasan suke da shi wajen jan ragamar jaririyar kasar ya cika.

Ana ganin nan gaba Najeriya za ta taka rawar gani a idon duniya wanda ya hada da samun ci gaban masana’antu da bunkasar tattalin arziki.

A haka kowace shekara ake gudanar da shagulgula duk lokacin da ranar ta kewayo don tunawa da nasarar ranar. Shugaba kan yi jawabi ga kasa, inda ake koya wa yara wato dalibai fareti, kowace makaranta ta nuna bajintarta a dandali, yayin da Gwamna da sarakuna da manyan mutane kan zo su ma su shaida. Akan ba da kyaututuka ga makarantun da suka zo na daya da na biyu da na uku, haka wadansu kan dage su karba a shekara mai zuwa.

Ranar ’yancin kai na tafe da wasu alamomi kamar kan sarki da duwatsu da wasu muhimman abubuwa masu nuna kasa da kishin mutane a duk lokacin da aka gansu ko ranar ta kewayo!

Ana rufe makarantu da ma’aikatu, a yi wasannin gargajiya da suka hada da kade-kade da raye-raye da sauran abubuwan nishadi na al’adun mutane mabambanta.

Akan yi bukukuwa a ofisoshin jakadancin kasar nan a kasashen ketare, har a kai dare, sannan a yi liyafa ta musamman. Kamar yadda a wasu jihohi akan sa yara su wanke kaya ko a dinka sababbi, ta haka dalibai kan yi zumudi a jajibirin ’yancin kai.

A yi wa gidajen gwamnati fenti, a taro tattabaru a keji ko kwantena, yayin da shugaba zai sako su su tashi, su shaki iskar ’yanci!

Akan yi taron a birnin tarayya, kuma gwamnoni kan yi nasu a jihohinsu. Akan nuna karfin soji tare da wasa da jiragen yaki inda za su rika shawagi a sararin samaniya, sannan a kawata birane da tutocin kasa don nuna kishi. Kuma tashohin talabijin kan yi shirye-shirye na nuna mazan jiya da irin gwagwarmayar da aka sha da ’yan mulkin mallaka.

A daidai lokacin da ake bukukuwan ranar ’yancin kai a gidajen gwamnati wadansu ’yan kasa na neman dama su sace takalma ko salula, wadansu na wasa da biri, wadansu na tunanin abin da za su ci, ana can ana shagali da kudade, wadansu kalilan na more tattalin arzikin kasar, a daidai lokacin da wadansu ke daka yaji!

Tunda magabatanmu sun samo mana ’yanci, wajibi ne mu tsare ’yancin nan, mu karfafa shi da kishin kai da neman ci gaban da aka yi fatan samu a tashin farko. Ta hanyar gina kasa da mutane ne za mu cika burinmu, ba wai tara abin duniya ba.

A yau ko daliban sakandare ba kowa ba ne ya san ranar da aka samu ’yancin kai! Sai ka iske ’yan makaranta ba su iya taken kasar ba, hatta ’yan siyasar. Ba su san magabata ba koda na yankinsu, shi ya sa wadansu suka dauka Aminu Kano wani dan kasuwa ne, attajirin mai makaranta da asibiti. Babu littattafan tarihin magabata a makarantun firamare da sakandare, ko dakunan kwana ba a sa wa sunayensu, wani lokacin a jiha ko shiyyarsu kadai ake samun tituna masu sunansu, kabilanci da bangaranci ya shigo, ta yaya za a yi kishin kasa?

Idan ana so a dawo da kishin kasa a zukatan mutane tare da sanin muhimmancin ranar ’yancin kai, dole a dauki mataki musamman ga dalibai a makarantu kamar haramta jinkirin zuwa makaranta ko fashi, yaki da satar jarrabawa. Sannan a tabbatar da cewa shugabanni a kowane mataki walau siyasa ko sarakuna ko malamai na nuna misalai nagari a duk mu’amalolin da aka yi da su.

Tutoci a gidajen manyan mutane ko fada da karrama wadanda suka dace, haka a rika ba mutane masu kima sarauta ko jami’o’i su ba su shaidar Dokta a bisa wata bajinta ko baiwa ba wai daga samun mukami ba, sai a bi mutum da girmamawa, bayan wani ma barawo ne da shi aka kashe kasar!

Sannan a hada baki da ’yan wasan kwaikwayo da marubuta ta hanyar dasa kauna ba kiyayya ba a tsakanin ’yan uwa, ’yan kasa, ko Musulmi da Kirista kowa ya san darajar makwabcinsa. Huldar kasuwanci ta gaskiya, ta yadda kada kabilanci ya kwace cinikin.

Daga karshe babu abin da kasar nan ke bukata da ya wuce addu’a daga bakunan yara da manya, musamman domin lumana tsakanin kabilu da addinai, ga shi mun tunkari shekarar zabe, ta yadda za a yi zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu ci gaba da kwankwadar romon dimokuradiyya.

 

Buhari Daure

buharidaure@gmail.com

Modoji, Jihar Katsina.

 

Leave a Reply