Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

‘Abin da a kawo tsaikon aikin titin Abuja-Kaduna-Kano’

Ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ba a kammala aikin sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano ba.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala duba aikin, babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Mahmuda Mamman, ya danganta jinkirin kammala aikin ga matsalar tsaro, musamman a wani bangare na hanyar.
A cewarsa, da an samu tsaro, dan kwangilar ya himmatu wajen kammala aikin gaba daya cikin wa’adin da aka ba shi.
Mamman ya jaddada kudirin ma’aikatar na bin ka’idojin ƴan kwangila tare da tabbatar da kammala aikin a kan kari a farkon shekara mai zuwa.
Ya bayyana cewa sun fara kai ziyarar aiki ne daga babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da nufin duba ci gaban da aka samu kawo yanzu.
A cewarsa, sun kasance a wurin don gane wa tare da magance kalubalen da ake fuskanta saboda su na bukatar ganin matsalolin da kansu.
Ya ce makasudin ziyarar shi ne duba kalubalen da ake fuskanta tare da nemo hanyoyin magance su, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.
Mamman ya bayyana jin dadinsa da ingancin aikin titin, sannan ya bukaci dan kwangilar da ya kammala aikin cikin wa’adin da aka kayyade.

Leave a Reply