Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

PDP ta kwace Zamfara a hannun Matawalle

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Zamfara ta bayyana Dauda Lawal Dare a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Dauda Lawal ya samu ƙuri’u 377,726 – inda ya yi nasara a kan gwamna mai ci Bello Muhammad Matawalle wanda ya samu ƙuri’u 311,976.

An dai kwashe tsawon lokaci ana tattara sakamakon zaɓen sanadiyyar jinkiri da aka samu.

Rahotanni da suka fito daga jihar sun ce an sace jami’an tattara sakamakon zaɓe a kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar, daga ƙaramar hukumar Maradun.

Sai dai an saki jami’an daga baya.

Leave a Reply