Siyasa

Ni al’ummar Bauchi za su zaba Gwamna karkashin PRP – Mukhtar Balewa

Mai neman takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PRP, Alhaji Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa ya sha alwashin lashe zaben Gwamnan jihar na 2019 da ke tafe.

Alhaji Mukhtar, wanda daya ne daga cikin’ ya’yan marigayi Firayi Minista, Sa Abubakar Tafawa Balewa, ya ce ya zabi Jam’iyyar PRP ce saboda ita ce jam’iyyar da ta cika dukkan ka’idojin da suka dace da wannan zamani.

“Kuma na shiga wannan gwagwarmaya ce domin kawo canji a Jihar Bauchi wanda ya gagari shugabannin baya. Don haka idan aka ba ni dama zan sauya tsarin siyasa da kuma jin dadin al’ummar jihar baki daya,” inji shi.

Dan takarar wanda ya ce ya gaji dukan manufofin mahaifinsa na siyasa da kuma na Malam Aminu Kano da kuma Alhaji Balarabe Musa, ya ce tsare-tsaren da magabatan suka bari tuni aka yi watsi da su, aka kama wadanda a yau suke wahalar da al’ummar kasar nan.

“Don haka ina da tabbacin zan yi amfani da kwarewar da nake da ita, wajen yi wa al’umma hidima ba tare da gajiyawa ba. Sannan zan samar da dukan yanayin da dan Adam zai rayu cikin walwala da wadata.

Za mu samar da nagartattun hanyoyi, mu kuma inganta hanyoyin kiwon lafiya da habaka harkokin noma da kuma farfado da ilimi. Kuma ina da tabbacin al’ummar Jihar Bauchi za su zabi Jam’iyyar PRP, don tabbatar da wannan ci gaba mai dorewa da muke fatan kawowa,” inji shi.

 

Leave a Reply