Kano Ayau Hausa, Siyasa

Gawuna ya taya Abba K. Yusuf murnar lashe zaben Gwamnan Kano

Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya taya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris.

A wani sako na murya ta manhajar WhatsApp, wanda kakakin sa, Hassan Musa Fagge ya saki a yau Laraba, Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida addu’ar cewa Allah Ya sa ya zama shugaba na gari.

A cewar Gawuna, tun bayan da hukumar zaɓe, INEC ta sanar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam’iyyar APC ta rubuta ƙorafe-ƙorafe kan cewa a yi duba a sakamakon zaɓen domin akwai kura-kurai.

Ya kara da cewa duk da wannan yunkuri da APC ta yi na a sake tantance sakamakon zaɓen tare da sake zabuka a wasu gurare, sai INEC ɗin ta baiwa Abba shaidar lashe zabe a yau Laraba.

“Sabo da haka, tunda hukumar zaɓe ta daɗa tabbatarwa da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP zaɓen a yau 29 ga watan Maris, to ina mai tunawa magoya bayan mu cewa tun a baya min yi addu’a cewa in alheri ne, Allah Ya bamu, in kuma babu alkhairi, Allah Ya canja mana da abinda ya fi alkhairi.

“Shi kuma wanda ya ci zaɓen, muna masa addu’ar Allah Ya sa ya zama shugaba na gari.

“Mu na yi wa magoya bayan mu godiya bisa fitowa da suka yi kazan su da matan su suka zaɓe mu. Mu na godiya kuma ina kira ga magoya baya da mu zamana masu yadda da ƙaddara.

“Mu ma addu’a Allah Ya sa mu zama masu biyayya ga shugabanci da kuma bin doka. Allah Ya bamu lafiya da zama lafiya,” in ji Gawuna.

Leave a Reply