Kano Ayau Hausa, Siyasa

Wike ya tsallake tantancewar zama minista

Majalisar Dattijan Najeriya ta fara tantance mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika mata don neman amincewarta kafin ya naɗa su ministoci.

Na farko a cikin mutanen da aka tura sunayensu su 28, shi ne Abubakar Momoh daga jihar Edo.

A matsayinsa na tsohon ɗan majalisar wakilai, Abubakar Momoh bai fuskanci tsauraran tambayoyi kafin Shugaban Majalisar Ɗattijai Godswill Akpabio ya buƙaci ya risina wa majalisa, ya wuce.

Mutum na biyu da ya bayyana a zauren majalisar, shi ne Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas.

Babu masaniya kan adadin mutanen da majaisar za ta tantance a Litinin ɗin nan, ranar farko da fara wannan aiki.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aika da ƙarin sunaye, kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya

Leave a Reply