GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

NDLEA ta fara gangamin yaki da miyagun kwayoyi a Masallatai

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta ƙaddamar da gangamin yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a masallatai a Jihar Katsina a jiya Litinin, a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke halartar guraren tafsiri da kuma shirye-shiryen buɗe-baki a jiyan.
Kwamandan hukumar a jihar, Mohammed Bashir tare da tawagarsa, sun je masallacin Abubakar Sadiq Juma’at da ke Filin Samji da kuma masallacin Juma’a na Rafukka, Kofar Sauri, duk a babban birnin jihar.
Da yake jawabi a masallacin Juma’a na Rafukka, Bashir ya ce gangamin na da nufin wayar da kan iyaye da matasa kan yadda a ke amfani da miyagun ƙwayoyi ta haramtacciyar hanya
“Dalilin kai kamfen din zuwa wuraren da ake gabatar da tafsirin da wa’azi na Ramadan shi ne saboda iyaye da matasa suna halartar taron,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa matakin zai taimaka wajen sanar da iyaye matakan da za su dauka kan ƴaƴansu na hana shan miyagun kwayoyi.
A nasa martanin, limamin masallacin Juma’a na Rafukka, Sheikh Husamat Katsina, ya ce irin wannan shiri abin farin ciki ne, “domin barazanar ta shafi kowa”.
Ya ce maganin matsalar ita ce dukkan masu ruwa da tsaki su hada kai don magance matsalar.
“Ya zama dole iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar an jagoranci matasa ta hanyar da ta dace, domin su ne shugabanni na gaba,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Leave a Reply