GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Mutanen Da Sojoji Suka Kama A Kaduna Ba ‘Yan Bindiga Ba Ne – ‘Yan Sanda

Jami’an sojoji da na ‘yan sanda a Kaduna sun bayyana cewa mutanen da aka gansu a wani hoton bidiyo sojoji sun kama su, ba ‘yan bindiga bane. Makiyaya ne da suka biyo sawun wasu mahara da suka yi musu barna tare da sace musu shanunsu.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewar mutanen ba mahara bane, makiyaya ne wadanda suka taka sawun barawo a garin Kakura dake karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna; an fahimci hakan ne a yayin zaman sulhu da aka gudanar tsakanin al’ummar Gwari da Fulanin yankin.

Zaman wanda ya samu halartar Kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan, Shugaban Karamar Hukumar Chikun Injiniya Salasi Musa da Dan majalisar Tarayya Ayuba Chawaza da Hakimin Kujama Stephen Ibrahim da kuma Babban jami’in Soja Laftanar Kanar D.O Igwilo.

Kwamishinan ‘yan sandar jihar Kaduna, Yekini Ayoku ya bayyana cewa dukkan al’ummar Gwari da na Fulani harin da ‘yan bindigar suka kai a yankin ya shafe su, harin wanda ya afku a ranar Asabar da ta gabata ya yi ajalin kanin Hakimin yankin mai suna Isiaku Karfe.

“Maharan sun kai wa unguwannin Fulani hari bayan sun farmaki Gwarawan, sannan sun sace shanun Fulani, sai ya zama al’ummar Gwari sun fita don farautar maharan, inda su ma Fulanin suka biyo sawun shanunsu da maharan suka sace, nan ne ‘yan banga suka kama wadannan makiyayan bisa zaton sune maharan.” inji Kwamishinan kamar yadda muka kalato daga Leadership Hausa.

Leave a Reply