Kano Ayau Hausa, WASANNI

Messi zai bar PSG

Lionel Messi, ya shirya barin Paris St-Germain a bazara, kasancewar ba zai yarda da wani tayi na sabunta kwantiraginsa a kungiyar ta Faransa ba. (Beteve, via Star)

Dan wasan na Ajantina ya zo kungiyar ta PSG ce daga Barcelona a bara, inda ya sha wahala matuka wajen nuna kwanjinsa a kakarsa ta farko a kungiyar.
Sai dai kasancewar dama kwantiragin shekara biyu ya shiga da kungiyar, dan wasan ya ki amincewa da tsawaita kwantiragin domin ci gaba da taka leda a kasar ta Faransa.
Ana tunanin Barcelona na zawarcin dan wasan, yayinda wasu suke tunanin zai tafi Amurka ne ko kuma ya koma kasarsa da taka leda

Leave a Reply