BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Babu jihar da ke da damar sayan makamai-Buhari

Fadar gwamnatin Najeriya ta warware zare da abawa game da dambarwar da ta taso kan bai wa gwamnatocin jihohi damar saye da kuma mika wa jami’an tsaro manyan bindigogi.

Damabarwar ta taso ne bayan da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yi ikirarin cewar gwamnati na nuna banbanci wajen aiwatar da wannan doka.

Sai dai fadar na cewa babu wata jihar kasar da aka ba izinin sayo makaman yaki masu sarrafa kansu domin raba wa kungiyoyinsu na samar da tsaro.

Fadar ta kuma ce an ba jami’an tsaro umarni su hukunta wadanda suka ki bin wannan umarnin.

Gwamnan ya zargi cewa ana bai wa jihar Katsina damar siyo makamai yayin da ake hana wasu.

Sannan ya kuma sha alwashin cewar gwamnatocin jihohin kudu-maso-yammacin kasar su ma za su sayo wa jami’an kungiyar tsaro ta yankin, wato Amotekun makamai.

Sai dai a wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta hannun mai bai wa shugaban kasar shawara kan yada labarai, Garba Shehu, ta ce batun nuna banbanci kan wannan doka ba gaskiya ba ne.

A tattaunawarsa da BBC Malam Garba Shehu, ya ce gwamnati ta dade tana nanata cewa babu mutumin da aka ba izinin mallakar bindiga iri samfurin AK-47 ko ma wata bindiga mai sarrafa kanta.

Ya ce sun fito da wannan magana ne domin dakile jita-jitar da ake yadawa, saboda gwamnatin Buhari ba ta bai wa kowacce jiha damar sayen makamai ba.

Ya ce irin wadannan maganganun ke haddasa fitina a kasar.

”Kuma duk wanda aka samu dauke da irin wannan makamai ko ya mayar hankali kwance ko kuma a makashi kotu.”

Sannan kakakin ya ce abu da ya kasance gaskiya shi ne taimakon da gwamnan Katsina ya nema na horar da jami’an ‘Civil Defence’ kusan 600 domin su koyi yadda ake amfani da bindiga amma ba mai sarrafa kanta ba.

Sannan ya ce an ba jami’an tsaro umarni su hukunta wadanda suka ki bin wannan umarnin.

Kakakin shugaba Buharin, ya yi kira ga jama’ar kasar da su guji mayar da batun tsaro ya koma tamkar na siyasa.

Leave a Reply