Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin da ya faru a kasuwar Sabon Birni da ke jihar KAduna domin gano haƙianin abinda ya faru, da kuma kamo wadanda ake zargi.
Cikin wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an ga yadda wasu da aka yi zargin sojoji ne sun kashe mutum uku tare da shanu a ƙalla 100 a kasuwar Sabon Birni da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi a jhar Kaduna.
To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Onyema Nwachukwu, ta jajanta wa iyalan al’ummar yankin Sabon Birni da mutanen da lamarin ya shafa, tare da alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
”Kuma duk jami’in da muka samu da hannu a wannan lamarin, to za mu ɗauki matakin da ya dace a kansa”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.