Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Kudin mazabu ba aljihun ‘yan majalisa suke zuwa ba – Shekarau

A Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci da a kara yawan kudin mazabu da ake bai wa ‘yan majalisun dokokin kasar.

Sanatan ya bukaci da a karawa ‘yan majalisa kudaden aikin mazabu.

A cewar Sanatan da ke wakiltar Kano ta tsakiya kudaden da ake ba su don aiwatar da ayyukan raya yankunan da suke wakilta bai taka kara ya karya ba, saboda haka ne ba a ganin tasirin ayyukan.

A wata zantawa da BBC, Malam Ibrahim Shekarau ya ce akwai rashin fahimta kan batun kudin na mazabu.

A cewarsa, wasu ‘yan Najeriya na da tunanin cewa kudin yana zuwa aljihun ‘yan majalisar ne, ba tare da fahimtar cewa aikinsu shi ne bin sawun kudin don tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan da aka tsara yi da su ba.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samar da wata hanya da za a rika bibiyar ayyukan da aka shata yi don ganin an aiwatar da su ko akasin haka.

Haka ma ya musanta kallon da ake yi wa wannan zubin na ‘yan majalisa a matsayin ‘yan amshin shata, inda ake zarginsu da amincewa da bukatun bangaren zartarwa ba tare da bin diddigi ba musamman kan abin da ya shafi kasafin kudi ba.

Sanata Shekarau ya bayyana cewa fahimtar juna ne yasa ba a samun matsala tsakaninsu da bangaren zartarwa, ba kamar majalisar da ta wuce ba inda aka rika samun rikici tsakanin bangaroran biyu.

Leave a Reply