Allah Daya Gari Bambam

Kilba: Kabila Daya, Mabambanta A Tsarin Zamantakewa

A yau mun kewa mun kuma kutsa cikin duniya inda muka yi kicibis da mutanen Kilba, filin namu zai sadaku ne da Al’ummar Kabilar “Kilba”.

Kabilar Kilba na daya daga cikin kabilun Karamar hukumar Hong na jahar Adamawa (wato Gongola)  na kasar mu Nijeriya.

Hoba manyan kabilu ne mazauna kan dutse.A cikin Kabilun kan dutsen akwai pella,gwaja,Hong,kulinyi,garaha,bangshika,miljili,gayajaba,gaya-maki,gaya-skalmi,gaya-gou,gaya fa’a,gaya jabba,ndlang,hyama,kinking,motaku,kwapor,za da kuma zibi har wa yau kaf a karamar hukumar ta Hong. A ko wace kabila na kan dutse wato hoba akwai mai mulki wato sarki wadda suke kira (TOL KORA MA)  KORAMA wato saman dutse sai shi kuma TOL wadda a baki akan ce TTLE da yake nufin sarki, shi dai wannan sarki TOL ana sanin sa ne ta sunan kabilar sa,a ko wace kabila akwai kayuka da dama da ke da hanyoyin sadarwa nasu na kansu,komai nasu na rayuwa a tsare yake rayuwa suke yi mai inganci da kuma dadi.

Shi TOL KORAMA yana da majalisar sa dake kunshe da su yaduma, midala, bira’ol, kadagimi, kadala, dzarma da kuma batari, majilisar ya danganta ne daga yanayin kabilar duk da akwai ‘yan abubuwa iri daya kaman duk ofishoshin na TOL akwai abubuwa iri daya.

A cikin mutanen Kilba, mace an santa ne da dogaro da kai babu ruwanta da neman taimakon iyaye ko kuma mijin ta,sannan ba ta bude cikin ta gaban kowa wato ba ta fadan damuwoyinta ga kowa, amma budurwan da za ta yi aure kan fadi abun da yake ranta game da zabinta, haka zalika matar da ki za ta iya bude cikin ta ko fadar damuwar ta cikin kawaye ko kuma cikin mutane masu shekarunta.

Mutane ne masu hadin kai, a karni na sha takwas Dakta Henry Barth (1965) matafiyi mutumin kasar Jamus ya samu kabilar ta Hoba a cikin yawace-yawacen sa a lokacin kabilun kaf na karkashin lemar FURKUDOL,a cikin rahotannin da Dakta Barth ya rubuta na tafiye-tafiyen sa ya yi magana a kan Hoba inda ya kira su da masarutar Arnan kan dutsen da babu kamar su wajen tsarin rayuwa da dabi’a kaf yammacin Sudan. Ya kara da cewa wannan masarauta ta yi kama da masarautar kasar Misra da kuma kasar turai a lokacin, masarautar ta kasu kashi kashi tare da membobin ta, membobin da ke shugabantan kasar kaf mutane ne daga gidan sarautar kasar.

Dakta Barth ya ci gaba da cewa ko wane wata Gwamnonin tare da Ministocin kasar kan tura bayanai zuwa wajen sarki dan jiran umarni ko kuma hukunci. Gwamnonin kaf Yirmawa ne da shallawa,Yirma daya ne daga kabilar udong tunda shi kadai ne sai ake kiran sa da yirma. Gwamnatin a tsare take daga kan Yirma wadda yake babban su gaba daya,udong gari ne da har yau ake kira da udong.  Shugabancin hoba ya rabu kashi biyu,akwai shi TOL wato sarkin su gaba daya sai kuma kula da kasar ya fada hannun Shallawa da yirmawa,Kula da tsakiyar kasar ta fada hannun membobin majalisar sarki TOL shi kauma majalisar ya hada da.

SABIYA- sabiya shi ne babban minister wato prime minister da kuma babban mai bada shawara na sarki.

BIRA’OL- bira’ol shi ne mataimakin  prime minister

MIDALA- midala ministan tsaro kuma sarkin yaki

KADALA- kadala shi ne sufeto general na yan sanda,shi yake da alhakin kamo mai laifi ko kuma ya tura a kamo.

DZARMA- ministern kula da sha’anin sarauta

BATARI- mai unguwan unguwannin sarauta

KADAGIMI- mai shari’a kuma manyan fada

YADUMA- shugaban majalisar tarrayya da masu bada shawara.

Da jimawa bayan sanin da mukayi  karni na 19  sananne ne wajen yake-yake da kuma Jihadin Fulani duk da haka tarihi ya nuna mana cewa Hoba ba’a taba cin su yaki ba, an yi hare hare da dama amma hakar ba ta cimma ruwa ba.  Duk da son yakin mutanen Hoba a wannan lokaci basu taba fita yaki ba sai dai sukan fita su yaki kananan kauyukan Fulani su kwace musu abubuwan arzikin su.  Sun yi kama sosai da mutanen Isra’ila na wancan lokacin da suke fita daga kasar Misra zuwa kasar su ta alkawari.

Mutanen Hoba basu ta a cin yakin ko’ina ba da ya zama gari ne yasan gar da mutanen jihadi sai ya zamana ranan kasuwa akan hadu da yan jihadi da kuma hoba a pella da mbilla Kilba ranan kasuwa aci tare a watse. Mutanen Kilba na kabilar Hong an sansu da bikin su na tiwe da ake kwana dari da ishirin cur ana yi,biki ne da ake sadaukarwa ga iyaye da kakanni,raye raye,wake wake da ganguna tare da kuma zagayen gari.  bikukkuna kamar su bikin kamun kifi na njuwa da ake yi a tafkin njuwa a garin yola, da kuma kamun kifi na yinagu da akeyi a michika na jawo hankalin mutanen ciki da wajen garin daga watar march har zuwa may ko wacce shekara.

BISO (Binne gawa)

Yadda ake binne masu sarauta ya banbanta da yadda Ake binne sauran talakawa. Ba kaman sauran talakawa ba idan mai sarauta ya mutu akan bisine shi ba tare da wani jinkiri ba washe gari da safe bayan mutuwan shi,akan wanke mamacin a masa sutura cikin manyan riguna uku ko hudu a kwantar dashi ya kwana a wurin bauta na bidigal,washe gari a kwantar Dashi a kabarin sa  zaune akan kujerun da aka daura akan capet kafan sa a daure akan wata kujerar kansa kuma a kishingide akan cushion ma tashin kai wadda ake sawa tsakanin kan da kuma jikin ramin hannun sa na hagu rike da wukan sarauta  wadda ake masa matashi da karfe hannun sa na dama kuma a barsa a sake,akan raba garkuwan sa biyu ya zauna ta ko wani bari akan daya kafan kuma an jikace su da takalmi da akayi da leda sa’annan a kawo bakin gawayin da surukin mai sarautar nan ya kona akan daura kwano na gongoni akan mamacin sai a daura dan kasa a kai saboda ya zauna hanyan da zai sada ka da kabarin ake rufewa da manyan tukwanen da ake juya su suke kallon kasa dama akan yi ramuka a jikin tukwanen da imanin wai an sake ran mamacin sannan wannan al’ada shi ma yakan sake ruwan sama amma su Kilba basa goyon bayan wannan akida na pabir,karen da yafi soyuwa a wajen mamacin ake kashewa a bunne shi a gefen mamacin bayan haka sai a yanka saniya a raba naman wa ko wani dan’uwa mata da maza na mamacin, akan yi shagalin sati guda yadda ake ci a sha giya a cikin kwana ukun karshe na bikin mutuwan Giyan da ake kwana hudu ana hadawa an lura da cewa lamba bakwai lamba ce da ake hada ta da shuwagabannin Kilba,sannan kuma lamba ce mai muhimmanci a wajen pabir,da suke bisine sarakunan su a zaune rufe da gawayi ba al’adar Kilba bane saka dawa a hannun mataccun sarakunan su ba kamar yadda yake a wajen su hona,gabin,yungar da Kuma Kilba haka zalika ba al’adar su bane kona mamaci a watsa toka akan shuka,ba sa kuma cire kan sarkin ba kaman gabin da yungur ba su a wajen su idan aka sake tono sarki ko aka bude makwancinsa to za’a samu bushewar kasa,babu wani abu da ake yankawa a kan kabarin sarakunan Kilba sai dai bayan shekara daya akan yanka namijin akuya wadda ake daukowa daga gidan mamacin a yanka akan kabarin a dafa naman a ci gaba daya iyalen gidan sa.  Bayan anyi haka za’a iya raba gadon sa wa magadan da ya bari sunce idan har ba’ayi wannan yanka ba aka raba gado to tabbas kuruwar sarkin nan zai addabi wadda suka raba. Dukka sarakunan Kilba ana bisine sune akan dutsen Hong,sannan dukka mazan gidan sarautar za’a birne sune adan kasa da kan dutsen kadan haka zalika manyan yara mata na sarki amma banda kananan.

In aka yi dubi ga yanayin mulkin su kuwa ba su dauki duk ikon sun bada wa mutum daya ba,mutanen Kilba jarumai ne masu ikon da baza su iya daukan mulki su ba mutum daya yayi ta juya su ba, dan haka ko wace mazaba takan dauki daya daga cikin yaran sarauta ta daura a matsayin wakilin ta in kuma yanayin mulkin bai musu ba sai su sauke shi su nemo wani dan sarautar su daura,yaran sarautar ana kiran su da shel su ake kaiwa duk wani kuka in abun ya fi karfin su sai a mika shi zuwa ga yerima ko kuma sarkin gaba daya wadda ya zama shine kotun koli tunda shi shel ba sarki bane wakili ne,a laifin kisa kuwa  ba’a kaiwa shel mutanen kanbi tsohuwar al’ada ne wadda dangin da aka musu kisan babu batun diyya rai ake biya da rai. Ya rage wa dangin da aka wa kisan su zabi wadda zasu kashe suma daga dangin wadda yayi  bayan yaya ko dan wadda aka kashe yaje ya dau fansa yakan dawo gida yayi kaman yana kukan karya su kuma mata suyi ta shewa in kuma kisan anyi shine ba da gangan ba Wadda ya faru sanadin farauta ko wani abu makamancin haka wadda yayi kisan kan dauko gawan ya kawo gida ya sayi rigan da da’a burne shi dashi aikin shell ne wannan da zaran an gane cewa kisar ba da gan gan bane akan biya diyya wadda ake bayar da da yarinya wa dan uwan wanda aka kashe saboda ta haifi da namiji ya zama fansan mamacin da zaran hakan ya faru yarinyan zata iya komawa gidan su in tana so ba ruwan babban sarki a cikin maganan,kaman in aka zo rikicin gado shi ne sarki yake sa baki inda yakan  bada shafa masu rikicin suyi rantsuwa dashi  sannan a saka su yin musabaha.

Addini                                                                           

Addinin kabilar shi ne addinin yaren su,wadda aka gina shi da yaren ko wacce kabila,al’adu da dai sauransu.  Mutanen Fulbe,bwatiye,Kilba da kuma chamba ma’abota addinin kiritanci ne da musulunci,sannan akwai masu addinin gargajiya kaman su bwatiye,Kilba  da kuma chamba.  Addini ya bada gudumawa sosai a wajen dai dai ta rayuwar mutanen, akwai abubuwan da ake ganin su zunubi ko kuma haramun a addini dan haka akayi hani ga mutanen akan furtawa ko aikatawa kaman su zagi da batanci da dai sauran mugayen kalamai musamman cikin mutane babu ko tantama addini ya bada daman fadan ra’ayi  a cikin gaba daya kabilun,mutum ana tsammanin ya tsaya akan addininsa tare da kare ta da kuma bayyanata a duk inda yake walau ciki ko wajen al’ummar sa.

Leave a Reply