Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

An kulle Rukunin Kantunan Jabi Mall na Abuja saboda da tsaro

Mahukunta a kantin Jabi Lake da ke Abuja, sun sanar da rufe wajen na wani ɗan lokaci, biyo bayan barazanar kai harin ta’addanci a babban birnin tarayya, FCT.

A tuna cewa Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da wata shawara kan harkokin tsaro, inda ya ja hankalin ƴan Nijeriya game da yiwuwar hare-haren ta’addanci a FCT, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

A wani mataki na gaggawa, kantin ya sanar da dakatar da ayyukan cinikayya sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Instagram: @jabilakemallnigeria.

A yayin da ya ke ba da hakuri kan rufewar da ta zo kwatsam, mahukuntan sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kare lafiyar masu sayayya da kuma ma’aikata.

Leave a Reply