Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

‘Mutum 850,000 ne suka fada talauci a bara a Ghana’

Babban Bankin Duniya ya ce ‘yan kasar Ghana kimanin 850,000 ne suka fada talauci a shekarar 2022 sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ta ayyuka.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ambato Bankin Duniyar a wani sabon rahotonsa mai taken: “Hauhawar farashi: Fayyace Yadda Hauhawar Farashi ta yi Tasiri a Kan Talauci da Samar da Abinci,” wanda aka kaddamar a Accra babban birnin kasar ranar Laraba.

Bankin ya ce matsin lambar da hauhawar farashi ta jawo ya yi sanadin tabarbarewar yanayin da ake ciki tare da ta’azzara talauci da rashin abinci a tsakanin ‘yan kasar ta Ghana.

Rahoton ya ba da shawarar cewa masu ruwa da tsaki wajen tsare-tsare su kara kaimi don farfado da tattalin arziki da warware matsalolin manoma da suka hada da saukar da farashin takin noma da kuma kara yawan shirye-shiryen taimaka wa mutane don kare marasa karfi daga fadawa matsaloli.

A wata hira da kamfanin dillancin labaran Ghana ya yi da wani babban kwararre kan tattalin arziki na Bankin Duniyar Paul Corral, bankin ya yi amfani da ma’aunan kudi ne wajen gano abin da iyalai ke kashewa duk shekara inda aka fahimci hauhawar farashi ta jefa mutane da yawa a cikin talauci kamar yadda TRT ta kalato.

Shi ma wani jami’in Bankin Duniyar Kwabena Gyan a wajen taron kaddamar da rahoton ya ce matsalolin tattalin arziki da aka fuskanta a 2022 musamman hauhawar farashi sun yi mummunan tasiri musamman a kan talakawa.

Ya ce nan da shekarar 2025 da ake sa ran kasar ta farfado daga rikicin tattalin arziki da take ciki a yanzu, za a shiga sarkakiya wajen dakile kokarin gwamnatin Ghana na rage talauci.

Dukkan masu ruwa da tsaki daga jami’an gwamnati da na hukumomin duniya da kwararru da suka halarci kaddamar da taron sun tabbatar da cewa akwai bukatar samar da shirye-shiryen taimakon manoma da fannin noma don rage tasirin talaucin a kasar.

Leave a Reply