Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Hisbah ta kama kwalaben giya 5,800 a Kano

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama wasu motoci uku makare da kwalabe 5,800 na kamru uwar laifi.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Haruna Ibn-Sina ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Kano yayin da yake duba motocin da aka kama a ofishin Hisbah.

Kakakin hukumar, Lawan Fagge, ya bayyana cewa an kama motocin uku ne a ranar Lahadi.

Motoxin sun haɗa da Mercedes Benz, wacce ke dauke da kwalaben giya 1,800; karamar motar Sienna, dauke da kwalaben giya 3,000 da motar Golf Volkswagen dauke da kwalaben giya 1,000.

Fagge ya bayyana cewa, Ibn-Sina ya yaba wa sashin hana ta’ammali da kayan maye da su ka damke motocin bisa kokarinsu na ganin an daina shan barasa da muggan kwayoyi a jihar kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.

Ya kuma ba da tabbacin hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta tsaftace jihar Kano daga duk wani nau’i na munanan dabi’u, musamman masu safarar miyagun kwayoyi da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“Hukumar Hisbah ta jihar Kano tana aiki tukuru don tabbatar da cikakken bin doka da ka’idoji, koyarwar Musulunci, kyawawan dabi’u, da zaman lafiya tsakanin kabilu da addinai,” in ji Malam Ibn-Sina.

Ya umurci sashen shari’a na hukumar da ya bi ka’ida ta hanyar mika kayan ga kotu domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply