Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Gobara ta tashi a Kasuwar Singa a Kano

Yanzu haka gobara ta tashi a wani shago da ke babbar kasuwar sayar da kayan masarufi wacce aka fi sani da Singa a Jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa wani shagon sayar da biskit da alawoyi ne ya kama da wuta a cikin gidan Nimza a kasuwar.

Wani ɗan kasuwar, Jamilu Zubairu ya ce wutar ta faru ne da misalin ƙarfe 9 na safe.

Sai dai ya ce yanzu haka jami’an hukumar kashe gobara sun je su na ta ƙoƙarin kashe wutar.

Leave a Reply