GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Francia Marquez: Kuyangar wani attajiri da ta zama Mataimakiyar Shugaban Kasa

Sakamakon zaben shugaban kasar Kolombiya na 2022 ya kasance na ban mamaki saboda dalilai da dama – tsohon dan gwagwarmaya Gustavo Petro ya zama shugaban kasa na farko  mai ra’ayin kawo sauyi kuma abokiyar takararsa ita ma ta kafa tarihi.

A ranar 7 ga Agusta, Francia Marquez, wadda matashiya ce kuma uwa, wacce a da ta kasance kuyanga da mai hakar zinare,  ta zama mataimakiyar shugaban kasa bakar fata ta farko a Kolombiya.

Marquez, mai shekaru 40, tana da kwarjini na musamman idan aka kwatanta ta da duk magabatanta.

Da farko, ba ta cikin tsarin siyasa da zamantakewar Kolombiya.

Kolombiya kasa ce  mai kabilu da al’adu  daban-daban kuma a al’adance ma’aikatunta sun kasance a hannun mazajen  birnin, masu arziki kuma  farar fata.

Amma sabuwar mataimakiyyar shugaban kasa ba ta gamsu da ƙimar kasancewa mace baƙar fata ta farko da za ta hau karagar mulki a karon farko ba.

Ta shaida wa BBC a wata hira da aka yi da ita a ranar 23 ga watan Yuni cewa “Ba wai na kawo kaina ba ne don na nuna fuskata a matsayin bakar fata ko na nuna kaina a matsayin mace ko kuma kawai na nuna cewa gwamnatinmu ta kunshi kowa da kowa”.

An haifi Marquez a Yolombo, wani kauye mai nisan kilomita 437 daga Bogota babban birnin kasar.

Kauyen na cikin Jihar Cauca daya daga cikin yankuna masu fama da talauci da kuma yawan kauyuka a kasar.

Haka zakalika rikicin da aka shafe tsawon shekaru 65 ana yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin sa kai da ‘yan tawaye ya shafi yankin Cauca sosai.”Alal misali an yi watsi da al’ummata na tsawon lokaci,” in ji ta.

“Babu ruwan sha da tsaftar muhali ko wutar lantarki.”

Marquez tana daya daga cikin yara 12 kuma ta yi rayuwa a shekarunta na farko ta hanyar yin aiki tare da iyayenta a wata mahakar zinare da ke bakin kogin Ovejas.

Tana da shekaru 16 ta haihu kuma ta fara aiki a matsayin ‘yar aikin gida — da ke wanke-wanke da sauran ayyuka — domin ta samu kudin kula da babban danta Carlos tare da biyan kudin karatu a Jami’a a fannin aikin noma- tana kuma da Digirin Digirgir da ta samu shekaru biyu da suka gabata a fannin aikin lauya.

Marquez ta kuma rika fafitukar kare muhali, ciki har da zanga-zangar nuna adawa da shirin karkatar da kogin Ovejas zuwa madatsar ruwan Salvajina a cikin shekarun 1990. Tana cikin wadanda suka rika gangamin da ya sa Kotun Kolin kasar ta dakatar da aikin.

Daga bisani ta jagoranci wasu da suka nuna turjiya a kan shirin gwamnatin tarayya na ba kamfanonin kasashen waje hakkin hako ma’adinai bayan ta kori bakar fata ‘yan Kolombiya da suka mallaki filayen hakar ma’adinai.

A 2014 tauraruwar Marquez ta haskaka inda ta jagoranci mata da dama a wani tattaki mai nisan kilomita 350 zuwa Bogota domin neman daukar mataki matsalolin da ake fuskanta a fannin zamantakewa da muhalli da hakar ma’adinai ba bisa kai’da ba a Cauca a lokacin mulkin Shugaba Juan Manuel Santos, kamar yadda muka kalato daga BBC.

Leave a Reply