Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Dalibai sun yi zanga-zanga a Bauchi don an raba mata da maza a makarantu

Daliban makarantun sakandire a jihar Bauchi sun fantsama kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da sabuwar manufar da gwamnati ta yi na raba maza da mata a makarantu.
Zanga-zangar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin dawo da makarantu a fadin jihar ranar Litinin.
Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen raba dalibai maza da mata a makarantun sakandare a jihar.
Tilde ya bayyana shirin ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan wani taron majalisar zartarwa ta jihar, SEC a Bauchi, inda ya kara da cewa sabuwar manufar za a aiwatar da ita ne kawai a duk lokacin da ta yiwu.
Ya bayyana cewa, manufar ita ce a magance tabarbarewar tarbiyya, wanda ya ce ya zama ruwan dare a tsakanin daliban makarantun sakandare.
A cewarsa, makarantu masu zaman kansu za su dauki matakin ne domin raba mazan da za su halarci ayyukansu na ilimi a wata cibiya da kuma mata a wata cibiyar daban.
Sai dai kuma gwamnatin Jihar Bauchi ta karyata rade-radin zanga-zangar Daluban Makarantar Sakandaren Jihar a Safiyar Yau Litinin, bayan da aka wallafa Hotunan ayarin Yara dalubai a sabbin kafafen sadarwa soshiyal Midiya.
Kafin yanzu maaikatar ilimi ta Jihar ta shelanta maido da tsohon tsarin raba dalubai Mata da Maza a Makarantun Sakandare, ko wane jinsi ya tsaya a bangaren sa.
Kwamishinan ilimin Jihar, Tilde, shine ya bayyanawa manema ta wayar tarho, yace suna kokarin tabbatar da tarbiyyar Yara masu tasowa a matsayin su na Iyaye ganin da kokarin kaucewa gurbacewar tarbiyyar zamani dake yin tasiri a wajen ‘yayanmu kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.
Yace ba zanga-zanga bace dokar ce ta fara aiki inda aka hada Daluban Makarantar Comprehensive dake bayan Tafawa Balewa Ested da Kuma Makaranta kofar Wamba’i, sai Daluban suke kallon Hakan a matsayin wani sabon abu.

Leave a Reply