Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Cristiano Ronaldo ya ki taya Messi murna

Cristiano Ronaldo, mutumin da yafi kowa magoya a shafukan sada zumunta har yanzu bai ce komai ba, tun bayan da Lionel Messi ya taimaki Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.

Argentina ta samu galaba a kan Faransa da ci hudu da biyu a bugun fenariti bayan sun buga wasa tsawon minti 120 kuma aka tashi uku da uku.

Masoya kwallon kafa sun ce ba a taba buga wasan da ya kayatar kamar wannan ba a tarihin gasar cin kofin duniya.

Ronaldo wanda magoya bayansa miliyan 780 ne jumlace a shafukan Twitter da Instagram da kuma Facebook, ya yi gum da bakinsa game da nasarar Argentina da Messi, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Har yanzu bai taya Messi murna ba a bainar jama’a.

Leave a Reply