Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Covid-19: ‘Mata miliyan bakwai za su samu ciki a duniya’

Hukumar Da Ke Kula da Yawan Al’umma Ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA, ta ce cutar korona za ta haifar da karuwar juna biyu da ba a shiryawa ba.

UNFPA ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar ranar Talata 28 ga watan Afrilu.

Hukumar ta yi hasashen cewa idan har aka yi wata shida cikin dokar hana fita, kusan mata miliyan 47 a kasashe masu karamin karfi ba za su samu kai wa ga hanyoyin da suka saba ba na matakan hana daukar ciki.

Hukumar ta ce a za a iya samun juna biyu sama da miliyan bakwai saboda kulle da al’ummar duniya suke ciki.

Ta kuma yi gargadi kan karuwar rikici tsakanin ma’aurata da za a iya samu sama da milian 30 a tsawon wannan lokaci.

Shugabar UNFPA Dr. Natalia Kanem ta ce: “Sabbin bayanan sun nuna irin bala’in da Covid-19 za ta iya jawowa mata da ‘yan mata nan kurkusa a duniya baki daya.

”Annobar na kara jawo rashin daidaito, miliyoyin mata da yara a yanzu suna fuskantar rashin yadda za su tsara iyalansu da kare jikinsu da kuma lafiyarsu.” Kamar yadda BBC ya ruwaito.

Leave a Reply