Kananan Labarai, Uncategorized

Bolsonaro ya kama hanyar lashe zaben Brazil

A ci gaba da zaben Shugaban Kasa a Brazil, Mista Jair Bolsonaro ya zarce abokin karawarsa na Jam’iyyar WP, Fernando Haddad, kamar yadda kafar labarai ta Reuters ta ruwaito a ranar Talatar da ta gabata.

Jadawalin hasashen zaben da kafar ta bayyana, ya nuna cewa Bolsonaro na iya samun kashi 44 cikin 100, yayin da Haddad zai iya tikewa da kashi 42 na kuri’un da ake ci gaba da kadawa a kasar, sannan ragowar kashi 14 za su iya lalacewa.

Amma idan babu wanda ya samu nasara a zagayen farko,  ranar Lahadin da ke tafe, to zaben zai zarce zuwa zagaye na biyu a ranar 28 ga Oktoba a tsakanin zaratan biyu.

Ana wannan hali ne a daidai lokacin da tsarin dimokuradiyyar kasar ya gamu da matsalolin rashin yarda daga jama’a, inda matsalolin cin hanci da rashawa da ake bankadowa tun shekarar 2014 musamman a kamfanin man fetur na kasa suka kara sukurkuta al’amura.

Kusan dukan manyan jam’iyyun siyasar kasar Brazil suna cikin wannan badakala da aka bankado. Kuma kashi 68 cikin 100 na mutanen kasar sun nuna rashin yarda ga jam’iyyun siyasar  kasar.

A cewar wani masanin dokoki Michael Freitas Mohallem, babu yadda za a yi dan takara Jair Bolsonaro ya raba kansa da abin da ke faruwa kamar yadda yake ikirari.

“Manyan jam’iyyu sun gaza sake sabunta masu rike da manyan mukamai na jam’iyyun. Kuma maganar samun wani sabon jini ya gaza samuwa. Bolsonaro wanda yake ikirarin sabon jini ne, shi kansa ya shafe shekaru ana damawa da shi a harkokin siyasa,” inji shi.

Daga cikin ’yan majalisa 513 da aka zaba a shekarar 2014, 36 ne kacal suka samu kuri’un da ake bukata, sauran sun samu ne bisa tsarin Brazil na cewa idan dan takara ya samu fiye da kuri’un da yake bukata sai jam’iyyarsa ta yi amfani da kuri’un wajen ceto wadansu ’yan takara.

Bisa tsarin Brazil sabon zuwa majalisa yana bukatar kimanin kuri’a dubu 116, sannan mai neman sake dawowa na bukatar kimanin kuri’a dubu 766, inda gabilin kudaden yakin neman zaben suke salwanta.

Leave a Reply