HANTSI, Kano Ayau Hausa

Boko Haram ta kashe mutum 30 a Borno

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum fiye da 30 a garin Auno na jihar Borno.

An kai harin ne da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, kamar yadda dan majalisar wakilai Satomi Ahmad ya shaida wa BBC.

‘Yan bindigar sun yi awon gaba da wasu da har yanzu ba a gano adadinsu ba, wadanda yawancinsu matafiya ne,

Dan majalisar ya ce ‘yan Boko Haram sun kona motoci kusan 20 kuma wasu akwai mutane a cikinsu, sannan kuma akwai mata da kananan yara a cikin wadanda suka yi awon gaba da su.

Garin Auno yana da nisan kilomita 24 daga babban birnin jihar Maiduguri.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zullum ya wallafa ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce gwamnatin jihar tare da gwamnatin tarayya na kara himma wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram a Maiduguri da kewayenta.

Auno shi ne garin da shingayen jami’an tsaro suke na karshe wanda daga shi sai shiga birnin Maiduguri.

Leave a Reply