Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Bankin Polaris ya hana ma’aikatansa Musulmi zuwa sallar Juma’a

Ma’aikatan bankin na Polaris na cikin fushin hana su zuwa sallar Juma’a da hukumar bankin suka yi a wani saƙo ta imel da aka aike musu a ranar Talata ta kafar imel.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan bankin ya tsegunta wa jaridar The Daily Reality cewa an gargaɗi wata ma’aikaciyar bankin kan hakan wadda mai kula da tafiyar da aikinta ya yi mata wanda shi kuma Kirista ne.

Saƙon imel ɗin yana ɗauke da saƙo kamar haka: “an fahimci cewa a ranar Juma’a kukan bar wuraren aikinku ku tafi sallar Juma’a duk kuwa da kun san irin tasgaro da kuma tsayawar aiki da hakan ke janyowa”.

“Ku sani cewa babu wata saɗara cikin ƙa’idojin bankin nan da ta ba wa ma’aikaci damar halartar wata sabga da ta shafi addini a cikin lokutan aiki”.

“Duba da haka, babu dama ga kowanne ma’aikaci da yake aiki a kowanne sashe na wannan banki na aikata hakan, duk wanda kuwa ya yi kunnen-ƙashi za a ɗauki matakin gaggawa a kansa”.

Wani lauya a Kano, Barista Abubakar Saleh, ya zanta da mai rahotonmu cewa wannan hani da bankin suka yi ya saɓa da ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba wa kowanne ɗan ƙasa na damar yin addininsa.

Haka ma wani malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Ayuba Tangimi, ya ce sallar juma’a wajibi ce ga kowanne musulmi. Malamin kuma ya ƙara da kawo wasu hujjoji cikin hadisai da maganganun malamai magabata kan wajibcin sallar Juma’a ga musulmi da kuma haɗarin da ke da akwai wajen ƙin yin ta.

Leave a Reply