Siyasa

Ban so aka saki bidiyon Ganduje ba- Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce ba zai mayar da martani ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba a kan zargin da ya yi cewa shi [Kwankwaso] ya kwashe kudin jihar ya yi yakin neman zabe a shekarar 2015.

Sanata Kwankwaso ya ce “ba zan ce komai a kan wannan zargi ba saboda shugaban kasa bai san komai a kan yarda muka tafiyar da mulki a Kano ba.”

Dan majalisar dattawan ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan rediyon Dala FM da ke jihar ta Kano ranar Talata da daddare.

Kwanakin baya ne lokacin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a kasar Faransa, ya shaida wa wani taron ‘yan Najeriya, ciki har da ‘yan jihar Kano, cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kammala ayyukan da mutumin da ya gada, Sanata Kwankwaso ya bari bayan da ya kwashe kudin jihar ya yi yakin neman zaben shugaban kasa a 2015.

Kwankwaso da Buhari na cikin mutanen da suka nemi tsayawa takara a jam’iyyar APC a wancan lokacin, amma Janar Buhari ya samu nasara.

“Mutane da yawa sun zo sun gaya min abin da shugaban kasa ya fada. Har bidiyon kalaman da ya yi suka kawo mini. Abin da ya sa ba zan ba shi amsa ba shi ne, ya yi maganganunsa ne kawai wadanda ya ji daga wurin mutanen da ke kewaye da shi. Bai san komai a Kano ba,” in ji Sanata Kwankwaso.

Ya kara da cewa Gwamna Ganduje bai ci gaba da ayyukan da ya fara ba, yana mai cewa “dukkan ayyukan da ya ci gaba da aiwatarwa “na gwamnatin Shekarau abokin Buhari ne.”

A cewar Sanata Kwankwaso, duk mutanen da ke zuga shugaban kasa domin ya bata masa suna ba sa kaunarsa.

Ya ce “sun je suna gaya masa cewa ni dan ta’adda ne, ba na son Buhari. Amma ina so ku sani cewa duk cikin wadannan mutane ba wanda yake son Buhari kamar ni domin ni na taimake shi [ya ci zabe].

Ganduje makiyi ne

A karon farko tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi tsokaci kan bidiyon da ke zargin gwamna Ganduje da karbar cin hanci na dalolin Amurka.

A cewar sa, “Kafin a fitar da bidiyon na samu labari, amma na ce kar su sake shi. saboda abin kunyar ba kawai na iyalin gwamna ba ne, abu ne da ya shafi martabar mutanen Kano da addininsu da kuma kujerar da na rike mai alheri.”

Sanata Kwankwaso ya ce dukkan mutanen Kano sun zama abubuwan kyama a idanun duniya saboda abin da ake zargin gwamnan jihar da aikatawa.

Ya ce gwamna Ganduje masoyinsa ne wanda ya rikida ya koma makiyi.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya sha alwashin yin aiki tukuru wajen ganin an sauya “wannan gwamnati rubabbiya.”

Ya ce ayyukan da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Alhaji Abba Kabir ya yi a lokuta daban-daban za su ba shi damar yin nasara a zaben 2019.

Leave a Reply