Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Ba zan taɓa raga wa ƴan ta’adda ba — Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta, yana mai cewa ko kadan bai zai raga wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a fadin kasar.

BBC Hausa ta tawaito cewa a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya fitar a jiya Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron kasar na iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar ‘yan bindiga a kasar.

Ya kuma jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe dan uwansa da ‘yan bindiga suka yi tare kuma da kame ‘yar uwarsa.

Yayin da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin makiya al’uma, Shugaba Buhari ya ce ya kadu matuka da wannan kisan

Ya kara da cewa ”Na yi matukar kaduwa da jijn labarin kashe dan uwanka, tare da kama ‘yar uwarka. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin-ciki”

”Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasarmu ke ciki”. In ji Buhari

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan ‘yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin kasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.

A cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha daya, an ga ‘yan bindigar na lakada wa fasinjojin maza dukan tsiya da ita ce.

Leave a Reply