GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Ba mu da kudin motar zuwa wajen aikin— Shugaban ASUU

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce mambobin kungiyar ka iya samun wahalar zuwa makarantunsu don ci gaba da koyar wa a yau Litinin saboda ba su da “kudin mota”.

Ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi yayin da ya ke magana kan batutuwan da su ka taso daga dakatar da yajin aikin da ASUU ta yi a wani shiri na gidan talabijin na Channels Television mai taken Sunday Politics kamar yadda BBC ta ruwaito.

Farfesa Osodeke ya ce ba kamar lokacin da malamai ke zama a gurare da ke kusa da harabar jami’o’in kafin a tafi yajin aiki ba, yawancin malamai a yanzu suna zaune nesa da harabar makarantun saboda yawancin makarantu ba sa iya samar musu da masauki.

Ya ce tunda har tsawon watanni takwas ba a biya su ba, zai yi wuya su iya biyan kudin jigilar kayayyaki zuwa makarantunsu domin koma wa koyar da ɗalibai.

“A makarantu a wancan zamani, kowane malami yana zaune a harabar jami’a kuma za ku iya tattaki zuwa ofishin ku, amma a kwanakin nan, malamai da yawa suna da nisan kilomita 20, 30 zuwa ofisoshinsu. Ta yaya za su iya biya kuɗin jigilar su zuwa aiki?

“Waɗannan su ne batutuwan da za mu fuskanta, waɗanda rassanmu ya kamata su koka a kai.

“Mu na sa ran gwamnati za ta biya kudinmu na albashi na watanni takwas domin wadannan mutane su koma bakin aiki yayin da muke tattaunawa kan sauran batutuwa.”

Da yake tabbatar da dakatar da yajin aikin, ya ce “mun dakatar da yajin aikin ne da fatan gwamnati za ta yi abin da ya kamata, kuma zuwa gobe idan jami’o’i sun bude, da fatan malamai za su koma bakin aiki.

“Mun dakatar da yajin aikin ne saboda biyayya ga hukuncin kotun masana’antu saboda ba a warware matsalar gaba daya ba, babu wata yarjejeniya da aka sanya hannu.

Leave a Reply