Kananan Labarai

Ba marabar Buhari da Abacha – Obasanjo

Takaddama ta sake kaurewa a tsakanin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo da Shugaba Muhammadu Buhari, bayan da Obasanjo ya ce mulkin Buhari bai da maraba da na Abacha saboda yadda Shugaban ke son ya lashe zabe ko ta halin kaka.

Obasanjo ya fadi haka ne a wata wasika da ya rubuta mai taken “Damuwa da kuma mataki,” inda ya zargi Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), cewa ta shirya yin magudi a zaben na bana. A cikin wasikar wadda ita ce ta biyu da Obasanjo ya soki Buhari,  ya bayyana Hukumar INEC da wani bangare na Jam’iyyar APC, tare da bayyana cewa APC na yin katsalandan ga harakokinta.

Obasanjo ya yi misali da zaben Jihar Osun da INEC ta ce ba a kammala ba, “Hakan ya tabbatar da INEC tana iya sanar da jam’iyyar da take so ta ci zabe ko da kuwa ta sha kaye ko kuma akwai matsaloli da za su iya sa a soke zaben ko ta ce sai an je zagaye na biyu,” inji

Sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su tashi tsaye a yaki gwamnatin Buhari kamar yadda aka yaki ta Abacha ta hanyar yin addu’o’i a masllatai da coci-coci.

 

Leave a Reply