Siyasa

Atiku ne zai magance yunwa a Najeriya- Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan Najeriya su zabi Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar a zaben 2019 domin shi ne zai magance yunwa.

Kwankwaso ya bayyna haka ne  a lokacin kaddamar yakin zaben shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato.

Kwankwaso ya tabbatar da cewa  Atiku Abubakar shi ne wanda zai inganta harkokin ilmi tare da samar da  hanyoyi da kuma asibitoci masu inganci a fadin Nijeriya.

Har wa yau Kwankwaso ya bukaci al’ummar Nijeriya  maza da mata su marawa Atiku baya domin zai habaka harkokin noma  da kuma taimakon al’umma.

Leave a Reply