Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

ASUU ta sake tsawaita yajin aiki

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya, ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take ciki.

ASUU ta yanke wannan shawarar ce bayan zaman Majalisar Kolinta a daren jiya, inda ta ce za ta cigaba da yajin aikin har sai an samu maslaha.

Idan ba a manta ba, a watan Fabrairu ne aka fara yajin aikin na gargadi, sannan ta tsunduma na sai baba-ta-gani a watan Maris.

Kimanin wata shida ke nan yanzu ana yajin aikin.

Leave a Reply