BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An sako ragowar fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

An sako dukkan fasinjojin da suka rage a hannun wadanda ke garkuwa da su bayan da aka sace su a watan Maris na wannan shekarar cikin wani jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja.

Gwamnatin Najeriya ce ta sanar da wannan labarin cikin wata sanarwa da Farfesa Usman Yusuf, sakataren wani kwamitin ma’aikatar tsaron Najeriya mai suna CDSAC ranar Laraba.

Ebola za ta iya sake barkewa a Najeriya-NCDC

“Ina mai farin cikin sanar da kasa da ma duniya cewa da misalin karfe 4 na yammacin yau Laraba 5 ga watan Oktoba 2022, kwamitin mutum bakwai da hafsan hafsoshin dakarun tsaron kasa Janar L. E. O. Irabor ya sami nasarar ceto sauran fasinjoji 23 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda na Boko Haram bayan da suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris na 2022.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan kasar na cike da godiya ga sojojin Najeriya a karkashin jagorancin hafsan hafsoshin sojojin kasar, wanda shi ne ya jagoranci aikin daga farkonsa har zuwa karshe. Haka ma, sauran hukumomin tsaro da ma’aikatar sufuri duka sun taimaka gaya wajen nasarar da muka samu a wannan aikin,” kamar yadda BBC ta ruwaito daga sanarwar.

Sai dai kawo yanzu babu rahotannin inda aka kai fasinjojin da aka sako, ko yadda aka iya karbo su daga hannun ‘yan Boko Haram din da suka yi garkuwa da su na tsawon fiye da wata shida.

Leave a Reply