Kano Ayau Hausa, RAHOTANNI

Ebola za ta iya sake barkewa a Najeriya-NCDC

Cibiyar Kula da Cutuka ta Najeriya ta yi gargadin cewa ‘yan Najeriya na fuskantar babban hatsarin kamuwa da cutar Ebola.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, shugaban NCDC, Dr Ifedayo Adetifa ya ce “hatsarin ya karu ne sakamakon yawaitar tafiye-tafiye tsakanin Najeriya da Uganda, musamman wadanda suke bi ta filin jirgin saman Nairobi, da wasu kasashen da suka hada iyaka da kasar Uganda.”

Dakta Adetifa ya bayyana cewa, yiyuwar yaduwar cutar a Najeriya biyo bayan shigo da kayayyaki ya yi yawa saboda taruka da tafiye-tafiyen da ke da alaka da siyasa, yuletide mai zuwa da kuma sauran bukukuwan addini a watannin karshen shekara.

Ya ce hukumar NCDC da abokan huldarta sun gudanar da wani bincike cikin gaggawa don yin nazari kan shirye-shiryen cikin gida, kuma sun fara sa ido da tantance fasinjoji a tashoshin shiga kasar, tare da bin wadanda suka taho daga Uganda ko kuma suka taso daga can, har tsawon kwana 21 domin sanin halin lafiyarsu take ciki

Leave a Reply