BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An bude gidan dirama na farko a Saudi Arabia

An buɗe gidan wasan daɓe da raye-raye a birnin Riyadh, an kuma gabatar da wasan farko a cikinsa.

Wannan dai na cikin shirin Yarima Mohammed bin Salman na mayar da masarautar ta daban ta fuskar jin dadi da kuma tattalin arziki.

Labarin da aka yi sunansa Zarqa Al Yamama na wasa shugaban wata ƙabila ta masu koren idanu, wata kyauta da aka yi musu tun gabanin zuwan addinin Musulunci cikin Larabawa.

Hasashen da ta yi na wani haɗari da za su fuskanta bai samu karbuwa ba a wajen al’umarta – wani labari da zai ja hankalin duniya kamar yadda Ivan Vukcevic shugaban gidan ya bayyanaAn samu wani kamfani daga Switzerland domin taimakawa wajen gudanar da wasan farkon da koyar da kiɗe-kiɗen Gabas ta Tsakiya na shekarun baya.

Lokacin da aka gabatar wa da Mista Vukcevic da kamfaninsa cewa za a buɗe wajen shekara biyu da suka gabata, ya yi matuƙar kaduwa tare da nuna shakkun ko hakan zai iya faruwa ta dadin rai.

Leave a Reply