Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

An kama mutum 50 kan rikicin siyasa a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a Najeriya ta ce ta yi nasarar kama mutane 50 da take zargi da bangar siyasa da kwace a yayin taron siyasa da aka gudanar na PDP a jihar ranar Lahadi.

“Babu wanda ya fi karfin doka kuma duk mukaminsa sai mun hukunta shi, don doka gaba take da kowa”, in ji kwamishinan ‘yan sanda na jihar Wakili Mohammed.

“Babu yadda za a yi a ce wasu tsuraru su ji sun fi karfin doka.

“Don haka mun hana yawo da kowane irin makami, kuma mun hana fita da ‘yan banga yawon yakin neman zabe.” inji Wakili kamar yadda BBC ta rawaito shi.

Har wa yau, ya kuma ce rundunar ‘yan sandan jihar za ta sanya kafar wando daya da masu sayar da kwaya da kayan maye a jihar. Wakili Mohammed ya ja hankalin iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu kan shiga bangar siyasa don guje wa fushin hukuma.

Yanayin siyasa a jihar Kano na kara munana duk da yarjejeniyar da yan takara suka sanya wa hannu kan yakin neman zabe da gudanar da zaben cikin lumana a jihar.

A ranar Lahadi ne ‘yan daba suka rika far wa mutane tare da yi masu kwace jim kadan bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kai jihar Kano domin yakin neman zabe.

Lamarin da ya jawo asarar rayuka da tare da ji wa mutane munanan raunuka.

Leave a Reply