Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

An dakatar da Sheikh Nuru Khalid saboda ya caccaki gwamnati

Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid kan hudubarsa ta ranar Juma’a.

Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa.

A cikin wani saƙo da shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya aika wa BBC, ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a.

Sanarwar ta ce: “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.”

 

“An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ‘yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.”

Leave a Reply