Kananan Labarai, Uncategorized

An aika wa Shugaban Amurka wasika dauke da guba

Hukomomi a kasar Amurka na ci gaba da binciken wata takardar sanya wasika wato ambulan da ke dauke da adireshin Shugaba Donald Trump na Amurka da aka samu tana dauke da gubar sinadarin risin, wanda ake zargin wasikar na daga wasu wasiku biyu da aka karbe a ma’aikatar tsaro ta Pentagon.

Sanarwar da Ma’akatar Tsaro ta fitar ta tabbatar da samun wasikar da ke da alamar tambaya, wanda aka aike zuwa ga Shugaba Trump ranar 1 ga Oktoban nan. Sanarwar ta kara da cewa, “Ba a fadar Shugaban Kasa ta White House aka karbi wasikar ba, kuma wasikar ba ta shiga fadar White House ba.”

Jami’an Ma’aikatar Tsaron Amurka sun shaida wa Muryar Amurka cewa, an samu gubar risin a jikin dukan wasikun da aka aike Ma’aikatar Tsaro daya da sunan Sakataren Tsaron Kasar Jim Mattis, daya kuma zuwa ga Shugaban Ayyukan Rundunar Mayakan Sama, Admiral John Richardson.

An kai wasikun ofishin Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka (FBI) domin kara bincike, kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaro, Kanar Rob Manning ya fada.

Wasikun sun isa ofishin rarraba wasiku na Ma’aikatar Tsaro da ke wajen ginin Pentagon ranar Litinin. Jami’an kare ma’aikatar suka gano gubar lokacin da suke binciken wasikun, saboda haka wasikun ba su shiga cikin Ma’aikatar Tsaro ba, inji jami’an.

Ana dai samun gubar risin ne a wani irin wake. Idan aka shake ta ko aka ci ko kuma aka yi wa mutum allura da ita bayan an sarrafa ta, tana iya kashe mutum a cikin sa’o’i arba’in da takwas. Bisa ga cewar cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Amurka, gubar risin ba ta da magani.

 

Leave a Reply