Kananan Labarai

Akwai bukatar karin hanyoyin magance talauci –Osibanjo

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce, gwamnatin tarayya tana ci gaba da bullo da hanyoyin da za a fitar da ‘yan Najeriya daga cikin kangin talauci.

Fitar da ‘yan Najeriya daga cikin talauci zai kawo wa kasar ci gaba ta fannoni da dama.

Osibanjo ya bayyana hakan ne lokacin da yake jagorantar zaman majalisar zartarwa da ake yi duk ranar Laraba a fadar shugaban kasa Abuja.

Mataimakin shugaban ya ce, gwamnatin tarayya ta damu matuka akan rage yawan talaucin dake damun ‘yan Najeriya, yana daya daga cikin ajandar da gwamnati ke son cimma.

Leave a Reply