Kananan Labarai

Abin da ya sa na je Kano- Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano kuma mai wakiltar mazabar Kano Tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yana gudanar da wata ziyara ta kwanaki irinta ta farko a jihar tun da ya bar kujerar gwamnan Kano.

Sanata Kwankwaso ya ziyarci birnin na Kano ne ba tare da sanar da cewa zai kai ziyarar ba, abin da ya zo wa magoya bayansa da dama ba zata.

Wasu dai musaman ‘yan Kwankwasiyya na cewa ziyarar ta Kwankwaso ta firgita gwamnatin Kano, ta Abdullahi Umar Ganduje.

To sai dai kwamishina watsa labaran jihar ta Kano Malam Muhammad Garba ya ce sam ziyarar ba ta dadasu da kasa ba.

Muhammad Garba ya ce duk wanda ya dubi ziyarar zai tabbatar da cewa ba ta yi armashi ba.

A cikin kwanakin, tsohon gwamnan ya ziyarci wasu wurare a birnin Kano domin yin ta’aziyya da kuma sada zumunci.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa lokaci ya yi da ya kamata a ce ya je Kano, kasancewar shekara uku ke nan rabonsa da jihar.

 

Leave a Reply