Kano Ayau Hausa

Zan iya magance matsalolin Najeriya-Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu wanda ya yi sallar Idi a birnin Lagos ya amince cewa Najeriya na fuskantar kalubale mai tarin yawa amma kuma a cewarsa yana kokarin samar da hanyoyin magance matsalolin.

A cikin sanarwar da ya fitar na taya musulmin Najeriya murnar Barka da Sallah, Asiwaju Tinubu ya ce “Dole ne mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu damar halartar wata Sallar Idi”.

Ya ƙara da cewa Allah ba ya ɗora wa mutum abin da ba zai iya ɗauka ba.”

“Allah Ya san halin da ƴan Najeriya ke ciki kuma zai kawo musu sauƙi.”

Sannan ya buƙaci al’umma da su yarda cewa ƙasar za ta gyara, su kuma haɗa hannu wajen cimma nasarar hakan.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta fara neman hanyar magance matsalolin da ke addabar kasar ta hanyar shawarwarin da suke samu daga wajen kwararru don gyara tattalin arziƙi da kuma kawarda duk wani cikas da zai hana bunƙasar Najeriya.

Leave a Reply