BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Za mu daukaka kara kan hukuncin kisan malaminmu —Daliban Abduljabbar

Almajiran Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin rataya kan laifin batanci ga Manzon Allah (SAW) suna shirin daukaka kara.

Almajiran fitaccen malamin mazaunin Kano, karkashin inuwar A’shabul Kahfi Warraqeem, Reshen Jihar Bauchi, sun yi zargin siyasa a hukuncin da aka yanke masa, saboda a cewarsu, malamnin nasu ya caccaki Gwamnan Jihar Kano, kan zargin almundahana.

“Ba mu gamsu da hukuncin ba saboda muna zargin akwai hannun Gwamnan Jihar Kano da wasu malamai da suka dade suna zaman doya da manja da shi (Abduljabbar), wadanda suka yi masa kagen yin batanci domin su kawar da shi daga doron kasa ta hanyar amfani da karfin kotu,” in ji mai magana da yawunsu, Abdullahi Musa a Bauchi.

Ya shaida wa manema labarai cewa, “Zargin batancin ba komai ba ne illa neman goga masa kashin kaji daga magauta, ciki har da Ganduje da wasu malamai da ke ganin daukakar da Abduljabbar ke samu a matsayin baraza a gare su.

“Shi ya sa suka jefe shi da yin batanci domin su ja masa bakin jini saboda su samu dalilin kawar da shi.

“Saboda haka mun yanke shawarar zuwa kotu ta gaba mu nemi ta soke wannan mugun hukuncin, tare da tabbatar masa da ’yancinsa, musamman na yin addini da bayyana ra’ayi kamar yadda kunin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

“Muna rokon Hukumar Kare ’Yancin Dan Adam ta Kasa, kungiyar Amnesty International, da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin gida da na kasa da kasa, da kuma lauyoyin kare hakkin dan Adam irin su Femi Falana, da mai rajin kare hakkin dan Adam, Ahmad Isa — Ordinary President, da sauransu, da su fito su yaki wannan zalunci da taron dangi da aka yi wa jagoranmu na addini, Sheikh Abduljabbar, ta hanyar sama mishi agajin shari’a,” in ji Abdullahi Musa kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Ya yi zargin hadin bakin Gwamnatin Jihar Kano da wasu malaman da ba sa shiri da Abduljabbar wajen hallaka shi a kan laifin da bai amsa ba.

Leave a Reply