Kano Ayau Hausa, Siyasa

Za a koma da gawar duk wanda ya kama shisshigi- Elrufai

Gwamna El Rufa’i da ke amsa tambayoyi a shirin Tuesday Live da ake gabatarwa duk ranar Talata kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa ya ce “ga wadanda ke kiran wani ya shigo don ya shiga tsakani a Najeriya, muna jiransa ya zo ya shiga tsakani.”

“Za a koma ne da gawarsu domin babu wanda zai shigo Najeriya ya fada muna yadda za mu tafiyar da kasarmu. Mun samu ‘yancin kai.”

“Muna kokarin yadda za mu tafiyar da kasarmu yadda ya kamata. Kuma mun san tarihin wadannan kasashen da suke kokarin koya muna wadannan abubuwan.”

“Mun karanta tarihinsu, kuma mun san matsayin ci gabansu. sun fuskanci wadannan kalubalen. Don haka kamata ya yi mu yi aiki tare. Mu ba juna shawara amma ba su karantar da mu ba, in ji El Rufa’i.

Leave a Reply