Kano Ayau Hausa, Labarai

Za a kara albashin ma’aikata a Najeriya

Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ƙarin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ƙasar domin rage raɗadin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ƙasar.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Villa.

Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ƙasar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ƙasar, kuma ana sa ran zai zo da buƙatar ƙarin albashin a shekara mai kamawa.

Da aka tambaye shi sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ”ƙwarai kuwa, wannan shi ne abin da nake faɗa cewa kwamitin albashi da shugaban ƙasar ya kafa na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumar albashin ma’aikata ta ƙasar”.

“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ƙarin albashin”, in ji ministan kamar yadda BBC ta kalato.

Kan batun albashin wata takwas da malaman jami’o’in ƙasar ke buƙatar gwamnati ta biya su kuwa, Ministan ya ce batun na gaban kotu.

Leave a Reply